<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Yaki yana nan gaba da Shaiɗan,
 Sai ka ƙarfafa cikin Yesu.
 Yafa makamai domin iko dai,
 Sai ka tsaya kan Maganarsa.

[V2]
 KORUS
 Ji, ƴan yaƙi ! Haɗa kai da Kristi!
 Tashi, shirya! Ba da shaidarsa!
 Ci gaba dai, raira waƙar yabo!
 Yesu Kristi Shugabanmu ne.

[V3]
 2) Ga maƙiyanmu, tsoro ba ma ji,
 Gaba za mu yi, Ubangiji!
 Ɗauki takobi, nuna haskenku,
 Yaƙin Yesu sai da nasara.
 Korus

[V4]
 3) Ya kai Allahnmu, ji kukanmu dai,
 Taimake mu da ƙarfinka,
 Yaƙi zai ƙare, za mu tatu can,
 Ka karƃe mu cikin hutunka.
 Korus</lyrics>
<title>Yaƙi Yana Nan Gaba da Shaiɗan LW292</title>
<hymn_number>292</hymn_number>
</song>